DA DUMI DUMINSA:

 RRR    Duk Wadanda Suka Cike Wannan Tsarin na RRR Kusan Shekara 2 Kenan Data Gabata.

Mal. Indai An tantanceka, Ka bada bayananka Daidai, Kuma An shigar dasu Daidai, Kawai kasha kuruminka.

Kana Cikin Wadanda zasu Rabauta da 75k da Gwamnatin tarayya take Gaf da fara bawa talakawan Kasa.

Haka Shima Wanda ya sami 5k A farkon Shirin da akayi na Gwaji da Kuma wadanda suka sami 30k da yawansu suma zasu amfana da wannan kudi da za'a sake bayarwa, Domin harda BAYANANSU ake tantancewa a yanzu haka.

Haka abin yake ga masu CCT PVHH Wadanda akayi na Gwaji Akaran farko da kuma Wanda aka zabi wasu jihohi akayi a online daga baya,

Wasu Da yawama anfara basu kudin tin abaya.

Wasu Kuma an bude Musu Account a Access Bank da Zenith Bank a Karkashin Wannan shiri, Wasuma har ATM 🏧 dinsu sun karba.

Wasu Kuma an Tantancesu amma ba'a Turo musu da account ba, Amma sunada yellow kati 🟡 A hannunsu, Wasu kuma suna da blue 🔵 din kati a hannunsu, Dukkansu suna ciki da Yardar ALLAH.

A Yanzu Haka ba'a bada Wani code Domin cike RRR ba Kuma ba'a fitar da Saban link ba, Amma akwai Waɗanda aka ware aka turasu garuruwan da aka zaba Domin daukar bayanan mutane Domin su shiga cikin wadanda za'a bawa wannan tallafi.

Wasu adadin kuma kai tsaye Gwamnoni aka bawa amatsayin kasan Mutanansa.

Koma Meye dai yanzu anzo gabar Karshe da ake sa ran duk masu rabo zasu amfana.

Dama zancanmu a kullum Shine" Idan kaji ana cike abu irin Wannan matukar daga gwamnati yake to ka cike shi.

Karka sawa kanka gaggawa bayan ka cike, Kaidai ka roki ALLAH da cewa" ta yadda komai DADEWAR da za'ayi daga karshe ka tsinci kanka acikin masu rabo shine yafi komai mahimmanci ba gaggawa ba.

ALLAH yasa muna daga cikin masu Raban amfana. Mb Muaz. 


Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

LABARAI DA DUMI DUMINSA;

News Flash